Kasar Cote d'Ivoire ta gudanar da bikin taya murnar cikon shekaru 53 da samun 'yancinta a ranar Laraba, a yayin wani babban faretin sojojin kasar a wani dandalin kasa dake kusa da fadar shugaban kasar dake birnin Abidjan, cikin wani yanayin ko in kula na mutanen wannan kasa. A gaban shugaban kasar Alassane Ouattara, manyan jami'an gwamnati da kuma baki, ayarin sojojin 36 ne suka fareti bisa amon kida na 'yan sandan kasar, jandarma, rundunar sojojin kasar (FRCI) da kuma garda sarki. A tsawon wannan fareti, jami'an kwastan, jami'an gandun daji, 'yan sanda, jandarma, sojojin kasa, sojojin sama da sojojin ruwa na hukumomin kasar da dama, tare da bataliyoyi, har ma da na makarantun horar jami'an tsaro ne suka nuna gwanintarsu a gaban mutanen da suka halarci wannan bikin kasa.
Abu sabo a cikin bukukuwan cikon shekaru 53 da samun 'yanci na wannan shekara, shi ne hirar da shugaba Alassane Ouattara ya kebe tare da manema labarai na kafofin gwamnati a ranar Laraba a lokacin shirin labaru na talabijin din kasar da yamma, maimakon gabatar da jawabi ga 'yan kasa da shugaban kasa ya saba yi a jajibirin irin wannan bikin kasa. Kasar Cote d'Ivoire ta tsaya karkashin uwar renonta wato kasar Faransa ta samu 'yancinta a ranar 7 ga watan Agustan shekarar 1960. (Maman Ada)