Kimanin daliban kasar Cote d'Ivoire ishirin ne za su samu damar cigaba da karatu mai zurfi a nan kasar Sin a cikin tsawon shekarar makaranta ta shekarar 2013 zuwa ta 2014 bisa taimakon gwamnatin kasar Sin. Sha biyu daga cikin daliban da suka taki wannan sa'a sun karbi a ranar Litinin a birnin Abidjan takardun sheda na shiga muhimman jami'o'in kasar Sin daga hannun jakadan kasar Sin daka kasar Cote d'Ivoire Zhang Guoqing, a gaban idon darektan sashen Asiya da yankuna teku na ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar Cote d'Ivoire, Andre Philippe Gause.
Wadannan dalibai za su cigaba da karatun samun digirin Bac da masta a fannonin harkokin kudin kasa da kasa, kimiyya da fasaha, kasuwanci, lissafi, kimiyyar muhalli, jarida, harkokin hada-hadar kudi, da na gyare-gyare. Jakadan kasar Sin dake Cote d'Ivoire, mista Zhang Guoqing ya kira ga wadannan matasa dalibai da su kasance masu hazaka a cikin wannan shekara ta cikon shekaru kusan talatin na huldar diplomasiyya mai kyau tsakanin kasar Sin da kasar Cote d'Ivoire.
'Ya kamata ku dauki nauyin da aka aza muku, domin nuna niyyarku, kun cancanci wannan kudin karatu, sannan kuma za mu iyar mika muku tutar sada zumunci dake tsakanin Sin da Cote d'Ivoire, ta yadda matasan kasashen biyu su kara fahimtar juna, su taimakawa juna tare wajen karfafa huldar abokantaka domin samun cigaba tare.' in ji mista Zhang Guoqing a gaban wadannan dalibai. (Maman Ada)