A wannan rana, mai magana da yawun jam'iyyar MDC-T, wadda ita ce jam'iyyar hamayya mafi girma a kasar, ya bayyana cewa, shugaban jam'iyyar kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai ya riga ya janye rokonsa na sake gudanar da babban zaben kasar daga kotun tsarin mulkin kasar. Dalilin da ya sa ya yi haka shi ne domin a ganin jam'iyyar MDC-T, yadda za a saurari rokon Mr. Tsvangirai a kotun zai yi kamar abun ba'a.
Har wa yau kuma kakakin ya ce, kusan babu yiwuwa ga jam'iyyar ta MDC-T ta samu hukunci mai adalci. Saboda kwamitin kula da harkokin zabe na kasar ya ki gabatar da muhimman bayanan da abin ya shafa, sa'an nan, kotun tsarin mulkin kasar ta ki sauraron abubuwan shaida da aka fada yayin da za a saurari rokon a kotun, don haka jam'iyyar MDC-T ta yi bakin ciki kwarai da gaske. (Tasallah)