Shugaba Putin na kasar Rasha ya ce, hadin kan kasashen 2 a fannin al'adu na taka muhimmiyar rawa a huldar hadin kai dake tsakaninsu wadda ta shafi manyan tsare-tsare.
Dalilin hakan ne, kasashen 2 suka shirya bukukuwa da dama a karkashin jigon al'adu a shekarun baya. Mista Putin ya ce a bara, an yi bikin shekarar yawon shakatawa a kasar Rasha ta kasar Sin, da ma sauran wasu bukukuwa da suka gudana inda duka sun kara fahimtar juna da amincewa tsakanin jama'ar kasashen 2, ta yadda aka samu karfafa tushen huldar dake tsakanin kasashen 2.
A cewar shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kasashen 2 sun kasance makwabta kuma kawaye. A wannan karo, shugabannin kasashen 2 sun cimma matsaya daya kan kokarin hadin kai a fannoni daban daban, don tallafawa yunkurin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasashen 2.(Bello Wang)