Sabon faraministan kasar Sin Li Keqiang tare da takwaransa na kasar Rasha Dmitri Medvedev sun dauki niyya a ranar Litinin na kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen nasu biyu a yayin wata tattaunawarsu ta wayar tarho.
Mista Medvedev ya taya murna ga sabon firayin ministan kasar Sin Li Keqiang, tare da bayyana cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping zai yi a nan gaba a kasar Rasha na nuna babban muhimmanci ga dangantakar manyan tsare-tsare tsakanin Rasha da Sin. Haka kuma ya bayyana niyyar yin aiki tare da Li domin bunkasa dangantaka mai tushe tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni.
Mista Li a nasa bangare ya nuna cewa, karfafa huldar ta manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu muhimmin mataki ne domin moriyar kasashen biyu, haka kuma zai taimakawa zaman lafiya, zaman karko da kuma cigaba duniya.
Ziyarar shugabn kasar Sin nan gaba a kasar Rasha za ta kara kawo sabon jini ga ingiza huldar kasashen biyu, in ji mista Li, tare da tunatar cewa, karfafa hulda da kasar Rasha na daya daga cikin muhimman ayyukan diplomasiyyar kasar Sin. (Maman Ada)