Wata tsohuwar babbar jami'ar MDD ta baiyana cewa, burin kasar Sin wanda shugaba Xi Jinping ke fifitawa ya dace da burin Afirka, domin kasar Sin da Afirka za su iya cimma bunkasa ta hanyar yunkuri bai daya.
Tsohuwar mataimakiyar magatakardan MDD Asha-Rose Migiro ta baiyana hakan ne cikin jawabi da ta gabatar a jami'ar Dar es Salaam dake kasar Tanzaniya.
Ta ce, burin kasar Sin ya samu kyakyawar karbuwa a Afirka domin yana nuna amfanin cimma nasarori baki daya kuma ya dace da manufofi da nahiyar ke fafutukar cimma nasara kansu, wato kamar kawar da talauci, bunkasar tattalin arziki, da kuma samun bunkasa mai dorewa.
Migiro ta ci gaba da cewa, cimma nasarori sakamakon hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu zai baiyana albarkatun tattalin arziki da nahiyar take da su. (Lami)