in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta yi maraba da ayyukan Sin a Afrika
2013-07-04 10:31:34 cri

Kasar Amurka ta yi maraba da ayyukan da Sin take yi a nahiyar Afrika, tana mai masa lakani da suna gina dangantaka da nahiyar domin magance matsalolin shiyyar.

A lokacin da yake bayani wajen bikin tuna ranar cika shekaru 237 da samun 'yancin Amurka, jakadan Amurka a kasar Kenya Robert Godec ya ce, Afrika tana da muhimmanci ga duniya baki daya, don haka ya kamata kasashe su hada gwiwwa da nahiyar. Yana mai bayanin cewa, Amurka ta samu kwarin gwiwwa na ganin yadda kasar Sin ta shiga cikin nahiyar ka'in da na'in, tana kawo masu cigaba.

Jakadan ya yi kira ga daukacin kasashe da su hada gwiwwa da Afrika domin samar da yanayin da za'a iya yin komai a bayyane ba tare da rufa rufa ba, wanda hakan zai kara janyo sauran kasashe su yi sha'awan zuba jari.

Kasar Sin dai ta zama kasa mafi girma da take huldar kasuwanci da kasashen Afrika a shekara ta 2009, inda a shekara ta 2012 ta zuba jari na kudi kimanin dala biliyan 198.5, kuma ana sa ran nan da shekara ta 2015, za ta zuba jarin kudin da zai zarce kimanin dala biliyan 380.

Jakadan ya ce, kasar Amurka da ta Kenya suna amfani da abubuwa iri daya masu ban sha'awa, sannan kuma shugaban kasar Amurka wanda shi ne 'dan asalin kasar Kenya ya damu kwarai da son ganin an yi hadin gwiwwa tsakanin kasarsa da Kenyan.

Jakada Godec ya ba da tabbacin cewa, kasarsa za ta yi aiki kafada da kafada da kasar Kenya don samar da cigaba a fannin tsaron yankuna, kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, kasuwanci, kiyaye muhalli, sha'anin mulki da dai sauransu.

A ranar Talata ne dai, shugaba Barack Obama ya kammala ziyararsa a kasashe uku na Afrika, inda ya yi alkawarin ba da tallafi kudin har dala biliyan 7 domin taimakawa ayyukan samar da wutar lantarki. Ziyarar da ake ganin wani yunkuri ne na kamo kafar Sin a ayyukanta a nahiyar, ko da yake shi Obama, a jawabinsa a wani taro a kasar Afrika ta Kudu ya ce, shigar da Sin ta yi a Afrika yana kawo cigaba ma nahiyar kuma wannan bai zama barazana a gare shi ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China