Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta baiyana ranar Talata cewa, ta damu matuka game da rahotannin dake nuna cewar, yawan wadanda ba su da muhalli da 'yan gudun hijira a kasar Afirka ta Tsakiya (CAR) na ta karuwa.
Mataimakin mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey ya baiyana yayin jawabin da aka saba yi ga manema labarai a kullum cewa, a cikin kasar Afirka ta Tsakiya kadai, akwai mutane da suka rasa muhallinsu guda dubu 206.
An samu barkewar tashin hankali a shekarar 2012 lokacin da gamayyar 'yan tawayen Seleka suka kai hare-hare. An kulla yarjejeniyar zaman lafiya a cikin watan Janairu, to amman 'yan tawayen sun kwace Bangui, babban birnin kasar a watan Maris, inda hakan ya tilasta shugaba Francoise Bozize ya gudu.
Del Buey ya ci gaba da cewa, tun tsakiyar watan Yuli, 'yan gudun hijira 4125 sun isa yankin Moissala dake kudancin kasar Chadi, inda ya ce, izuwa yanzu akwai 'yan gudun hijira 62,700 da suka tsere zuwa kasashe dake makwabtaka da kasar, tun bayan barkewar rikici a cikin watan Disamban da ya gabata. (Lami)