Kakakin MDD Martin Nesirky ya fada a ranar Talata cewa, babbar jami'ar hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD Valeire Amos za ta ziyarci jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, don tattauna yadda za a kara taimakawa kasar ta fuskar harkokin jin kai.
Valeire Amos wadda ita ce mataimakiyar babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai, za ta fara rangadin kwanakin biyu a kasar ce daga ranar Alhamis, inda Kristalina Georgieva, kwamishinar EU mai kula da hadin gwiwar kasa da kasa, tallafin jin kai da mayar da martani kan rikice-rikice za su rufa mata baya.
Kakakin na MDD ya ce, ana sa ran Amos za ta tattauna da hukumomi da sauran abokan hulda da ke bayar da agaji kan harkokin jin kai game da hanyoyin karfafa bayar da tallafin jin kai a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A ranar Jumma'a ne aka shirya Amos da Georgieva, za su je Kaga da ke lardin Nana Gribizi, don game wa idonsu tasirin da rikicin ya yiwa harkokin jin kai da kuma kokarin bayar da agajin da ake yi a wurin. (Ibrahim)