Cibiyar harkokin tallafawa bil-adama ta MDD ta sanar ranar Talata cewa, an samar da dalar Amurka sama da miliyan 7.1 don samawa jama'a da yawansu ya wuce miliyan daya, wadanda mafi yawansu yara ne, tallafi na ceton rai, a jamhuriyar demokradiyar Congo CAR.
Ofishin gudanar da harkokin tallafawa bil-adama na MDD (OCHA), ya bayyana cewa, wadannan kudade da aka karbo daga asusun ba da agajin gaggawa na MDD (CERF), zai baiwa ma'aikatan ceto bil-adama damar samar da tallafi na kayan abinci da magunguna, ruwan sha da tsabtace muhalli, ga wadanda rikici ya ritsa da su, gami da ayyukan kula da shara da kiwon lafiyar haihuwa, in ji mai magana da yawun MDD, Martin Nesirky yayin jawabi ga manema labarai da aka saba yi yau da kullum.
Daga cikin mutane miliyan 1.1 da ake sa ran taimakawa, akwai yara kanana 595,000, 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa, in ji cibiyar ba da tallafin.
Yanayin zaman jama'a ya kara tabarbarewa ne a CAR tun bayan sake barkewar fada a watan Disamban 2012, wato lokaci da dakarun Seleka suka kaddamar da hare-hare.
An rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya ranar 11 ga watan Janairu a Lebreville,babban birnin kasar Gabon, inda aka cimma tsagaita bude wuta da kuma kafa gwamnatin hadin gwiwa ta hadin kan kasa inda aka baiwa 'yan tawayen muhimman mukamai, to amma kuma a cikin watan da ya wuce, 'yan tawayen sun sake kwace birnin Bangui bayan wani kazamin fada, inda hakan ya sa shugaban kasar Francoise Bozize ya tsere daga kasar.(Lami)