Tuesday    Apr 29th   2025   
in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da yankunan kudancin Sahara na Afrika za su tattauna cigaban AGOA
2013-08-13 10:32:51 cri

An bude wani taron tattaunawa a ranar Litinin 12 ga wata tsakanin kasar Amurka da na yankunan kudancin Sahara na nahiyar Afrika domin tattauna yadda hidimar kasuwanci da hadin kan tattalin arziki da aka fi sani da AGOA a Turance zai habaka, in ji Michael Forman, wakilin kasar Amurka a wajen taron.

Da yake bayani ga manema labarai game da jadawalin babban taron na wannan shekarar da za'a yi a kasar Habasha, Mr. Forman wanda har ila yau zai jagoranci tawagar da za ta halarci taro na Habashan, ya ce, jami'ai daga Amurka da ministoci na wadannan kasashe na Afrika sun rika sun kaddamar da jadawalin tsarin da za'a bi na yi wassu sauye-sauye ga cibiyar domin ta samu zuwa gaba. AGOA dai shi ne cibiyar samar da dabaru na tattalin arziki na hadin gwiwwa da yankunan kudancin Sahara na nahiyar Afrika, wadda ke da alhakin samar da iznin shigar da kayayyakin bukata daga Amurka guda 7,000 ba tare da haraji ba ga wadannan kasashen.

Wannan izini da aka bayar tun daga shekara ta 2000 zai kammala aikinsa ne a shekarar 2015, AGOA ta amince ma kasashen Afrika 39 da suka cancanta su ma su shigar da kayyayyakin bukatar ba tare da haraji ba ga kasar Amurka.

Kasar Habasha ce ke daukan nauyin shirya babban taron na 12, karkashin taken habaka sauye-sauye ta hanyar ciniki da fasasha. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China