Daya daga cikin gyare gyaren da aka tsaida kan dokar kwastan, wannan mataki na nuna niyyar hukumomin kasar Kamaru na rage tallafin gwamnati ga kamfanin tatar mai na SONARA domin taimakawa farashin man fetur a gidajen shan mai in ji shugaban gwamnatin kasar a yayin da yake gabatar da jadawalin kasar na gaba kan tattalin arziki, kudi, al'umma da kuma al'adu a zauren wakilan kasar.
Kasar Kamaru karamar kasa a wajen fitar da man fetur, tana fitar da gurbataccen man ne kawai, rashin sarrafawa a gida na sanya kasar sayar da shi kai tsaye a kasuwannin duniya, matsalar dake tilastawa wannan kasa dake tsakiyar Afrika sake odar man domin bukatunta na cikin gida daga kasashen Najeriya da Guinee Equatoriale dake makwabtaka da ita.
Yawan man fetur da kasar ke shigo da shi ya kai lita miliyan 131 a kowane wata, sannan bisa manufar tallafawa farashi a gidajen shan mai, gwamnatin kasar tana zuba kudin tallafi a kowane wata kusan biliyan 27 kudin Sefa kimanin dalar Amurka miliyan 54 in ji ministan kudin kasar mista Essimi Menye.(Maman Ada)