Labarin da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhua) ya samu a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba ya nuna cewar, a zaben shugaban kasar da aka yi ranar tara ga watan, shugaba mai ci Paul Biya na Kamaru, shi ne wanda madaukakiyar kotun kasar dake tsakiyar Afirka ta sanar an sake zaba, a sakamakon da ta fitar a hukumance ranar Juma'ar.
Paul Biya dai, da ma shi ne dan takarar jam'iyyar dake mulki a kasar Kamaru ta Democratic Rally for Cameroonian People (RDPC).
Mutane miliyan bakwai da rabi ne 'yan kasar Kamarun daga lardunanta goma, suka yi rijistar kasancewa cikin zaben. (Garba)