in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarihin wasannin Olympics
2013-08-01 20:18:10 cri

Dukkan 'yan wasa da suka halarci wasannin a wancan lokaci, ba su sanya kome a jikinsu, wannan ita ce alamar wasannin Olympics na wancan lokaci. Duk dan wasan da ya yi nasara a wasa, zai samu lambar yabo, kana za a rubuta sunansa a jikin katangar filin wasa. Idan har dan wasa ya yi nasara a gasar sau uku, za a gina mutum-mutuminsa don a karrama shi.

A lokacin, 'yan kasar Girka maza suna da iznin halartar wasannin Olympics, bayi, 'yan kasashen waje da kuma mata ba za su shiga wasannin ba. Bisa ka'idojin wasannin Olympics na lokacin da, an ce, idan aka gano mata suna kallon wasannin Olympics, hakika za a yanke musu hukuncin kisa.

Amma a lokacin da daular Sparta ta fi karfi, kanwar sarkin Sparta ta keta ka'idojin wasannin na Olympics inda ta halarci gasar wasan keken dawaki, har ma ta yi nasara a gasar, don haka ta zama mace ta farko da ta yi nasarar lashe wasa a tarihin wasannin Olympics. Daga nan ne, matan kasar Girka suka fara shiga wasannin mata da sunan "tunawa da gunkin mace mai suna Hera".

An gudanar da wasannin Olympics karo na 287 a lokacin. Bayan da Kristoci suka mamaye dukkan nahiyar Turai a karni na 2, sun yi watsi da wasannin motsa jiki, don haka aka dakatar da yin wasannin Olympics. A shekarar 394, sarkin Rome na wancan lokaci ya bada umurnin soke wasannin Olympics. Don haka, aka kawo karshen wasannin Olympics na lokacin.

Bayan da aka dakatar da gudanar da wasannin Olympics har na tsawon shekaru fiye da dubu 1, an sake maido da gasar a karshen karni na 19.

A karshen karni na 19, an samu babban ci gaba a fannonin tattalin arziki da al'adu a kasashen Turai, kana an kara yin mu'amala a tsakanin kasa da kasa, don haka aka fara yin mu'amala a fannin wasannin motsa jiki. 'Yan nahiyar Turai mutane ne masu son kiyaye zaman lafiya a nahiyar, kuma a ganinsu dawo da gasar wasannin Olympics shi ne hanya mafi kyau wajen samun zaman lafiya. Don haka, wani dan kasar Faransa mai suna Pierre de Coubertin ya yi kira da a sake dawo da gasar wasannin Olympics.

An haifi Coubertin ne a shekarar 1863 a birnin Paris dake kasar Faransa. Tun daga lokacin kuruciyarsa, ya ke sha'awar tarihin kasar Girka ta lokacin da sosai, don haka ya yi kokarin ganin an sake dawo da gasar wasannin Olympics.

A shekarar 1883, ya gabatar da shirin gudanar da wata gasa mai kama da gasar wasannin Olympics na lokacin da. Kuma a shekarar 1892, ya kai ziyara a kasashe da dama na nahiyar Turai don yada tunanin gasar wasannin Olympics. A shekarar 1893, ya gudanar da taron wasanni na duniya karo na farko don sake dawo da gasar wasannin Olympics. Kuma a shekarar 1894, ya sake gudanar da irin wannan taron a birnin Paris, inda aka tsaida kudurin kafa kwamitin shirya gasar wasannnin Olympics na duniya dake kunshe da kasashe 12. Kana an tsaida kudurin gudanar da wasannin Olympics na zamani karo na farko a birnin Athens dake kasar Girka a shekarar 1896.

An kafa cibiyar kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya a birnin Lausanne dake kasar Switzerland. Kuma burin gudanar da wasannin shi ne taimakawa dan Adam wajen gina duniya mai zaman lafiya da sa dukkan jama'a daga kasa da kasa su kara yin mu'amala da sada zumunta a tsakaninsu. Kuma babban taken gasar wasannin Olympics shi ne "kara sauri, tashi tsaye, da kara nuna karfi da kwarewa".

Launin tutar gasar wasannin Olympics fari ne, kuma akwai zobba biyar a kanta, wadanda ke da launin shudi, rawaya, baki, kore da kuma ja. Kuma an fara yin amfani da tutar ce tun daga shekarar 1920 wato lokacin da aka gudanar da gasar wasannin Olympics karo na 7. A lokacin, an bayyana cewa, wadannan zobba biyar su ne a madadin nahiyoyi biyar na duniya. Bayan hakan, an yi bayani da cewa, alamun zobban ko kawanya biyar sun wakilci dukkan launukan kasashe membobin kwamitin dake shirya gasar wasannin Olympics na duniya.

A halin yanzu, akwai wasannin Olympics iri guda biyu, wato na lokacin zafi da na lokacin sanyi. Ana gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin zafi a bayan shekaru hudu-hudu. Kana birni ne ke daukar bakuncin gasar wasannin, ba kasa ba. Sannan an amince da birane fiye da daya daga wata kasa su nemi iznin gudanar da gasar wasannin Olympics din, kuma tilas ne kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya ya zabi wani birni shekaru 6 kafin a gudanar da gasar. Kana tilas ne a gudanar da wasannin a cikin kwanaki 16.

A gasar wasannin Olympics karo na farko da aka gudanar a shekarar 1896, 'yan kasar Girka sun ci gaba da bin ka'idojin wasannin Olympics na lokacin da, inda suka ki amincewa da mata su halarci wasannin. Amma a karo na biyu na wasannin da aka gudanar a shekarar 1900, a karo na farko ne mata suka samu iznin halartar wasannin Olympics. A halin yanzu, yawan wasannin da mata ke fafatawa a gasar yana karuwa, kuma yawan 'yan wasa mata da suka halarci wasannin Olympics ya karu sosai.

Ban da wasannin Olympics na lokacin zafi da na lokacin sanyi, an kara gudanar da wasannin Olympics na nakasassu don kara yada tunanin wasannin Olympics. (Zainab)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China