in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin da ake ciki wajen share fagen wasannin Olympics na London
2011-12-14 17:29:07 cri

Ran 11 ga wata a ofishin jakadancin kasar Birtaniya dake kasar Sin a nan birnin Beijing, shugaban kwamitin wasannin Olympics na birnin London na shekarar 2012 Sebastian Coe ya yi bayani kan yanayin da ake ciki wajen share fage ga gasar wasannin Olympics na London, inda Mr. Coe ya bayyana cewa, wasannin Olympics na London za su ba da kyakkyawar dama ga 'yan wasa har ma ga masu yawon shakatawa domin su gano al'adu da wasanni iri daban daban na kasar Birtaniya.

Ban da haka, Sebastian Coe ya ce, ya fi sanin dan wasa na kasar Sin Liu Xiang, domin ya kasance zakaran wasannin Olympics har ma na duniya, kana ya taba karya matsayin bajinta na duniya sau da dama. Ya yi imani da cewa, Liu Xiang zai samu goyon baya da karbuwa daga masu sha'awar wasanni a birnin London. Kamar yadda Coe ya bayyana, a bangaren wasan kwallon kafa na gasar wasannin Olympics ta wannan karo, ba za a samu kasancewar kungiyoyin Ingila, Scotland, Wales ,da Northern Ireland ba, domin za su hada kansu su kafa kungiyar Birtaniya ko UK.

A ganin Mr Coe, kungiyar UK tana da kwazo, ganin yadda za a zabo 'yan wasan kungiyar daga kungiyoyi masu karfi dake Ingila, Scotland , Wales, da Northern Ireland, kana tsohon mashahurin dan wasan kwallon kafa na kasar Birtaniya Pierce zai zama mai horas da 'yan wasan kungiyar UK.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China