in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila wasan kokawa dawo cikin jerin wasannin Olympics
2013-06-13 09:30:31 cri
A kwanakin baya ne aka kammala taron kwamitin gudanarwa na hukumar harkokin wasannin Olympics ta duniya a kasar Rasha. Bayan kammalar taron, shugaban hukumar Jacques Rogge, ya gudanar da taron manema labaru, inda ya amsa tambayoyi game da shugabancin hukumar a karo mai zuwa, da batun dawowar wasan kokawa cikin jerin wasannin Olympics da dai sauransu.

Yace kwamitin gudanarwa na hukumar harkokin wasannin Olympics ta duniya ya jefa kuri'u, an kuma zabi kwallon gora ta baseball, wasan squash, da kuma kokawa a cikin jerin sunayen wasannin da watakila za su sake dawowa cikin jerin wasannin Olympics. A gun taron, akwai wasanni 8 da suka shiga takara, kuma daya bayan daya aka yi bayani ga kwamitin gudanarwar hukumar harkokin wasannin Olympics din ta duniya. Sa'an nan baya ga shugaban hukumar Rogge, sauran membobin kwamitin 14 sun jefa kuri'u. Inda nan take wasan kokawa ya zama na farko da ya shiga jerin sunayen wasannin da aka kadawa kuri'ar.

Yanzu dai haka a watan Satumbar dake tafe ne ake sa ran, hukumar za ta sake jefa kuri'u kan wadannan wasanni 3 da a yanzu suka same amincewa, za kuma a zabi daya domin ya sake dawowa cikin wasannin na Olympics. Idan wasan kokawa ya cimma nasara, za a dakatar da shirin shigar da wani sabon wasa a wasannin Olympics.

A gun taron manema labaru, Rogge ya bayyana cewa, wadannan wasanni 8 suna da kyau, akwai wuyar gaske a iya zabar wani guda daga cikinsu. Duk da hakan yace ba abu ne mai yiwuwa ba, a iya amincewa da dukkansu su shiga wasannin na Olympics. Ana bukatar tantance yawan wasanni da mutanen da za su shiga wasannin Olympics zasu iya takara a kan su. Ya ce, a wasannin Olympics na shekarar 2020, yawan wasannin ba zai wuce 28 ba, kana yawan 'yan wasa da za su shiga wasannin ba zai wuce 10,500 ba.

Shugaban hukumar na yanzu Rogge zai bar mukamin sa nan da watanni 3 masu zuwa. Ya zuwa yanzu, akwai mutane 6 da suka shiga takarar zama sabon shugaban hukumar. Mutanen kuwa sune memban kwamitin gudanarwar hukumar harkokin wasannin Olympics Sergey Bubka, da mataimakin shugaban hukumar Thomas Bach, da mataimakin shugaban hukumar Ng Ser Miang, da kuma shugaban kwamitin kudi na hukumar Richard L. Carrion. Ragowar sun hada da shugaban hukumar hadin gwiwar wasan dambe ta duniya Wu Jingguo, da kuma babban sakataren hukumar wasan kwale-kwale ta duniya Denis Oswald. Game da mutanen 6, Rogge ya bayyana cewa, dukkansu suna da kwarewa, ya nuna kyakkyawan fata ga duk wanda zai maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban hukumar.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China