Kamfanin Shell ya sanar da cewa, sakamakon wasu dalilan da ke shafar aikin fitar da man fetur, kamfanin ya yi shirin rufe wani bututun man fetur dake kasar, don gyara barnar da 'yan fashi suka yi wa bututun man fetur. Haka kuma, a ranar 23 ga wata, kamfanin ENI ya sanar da cewa, sakamakon harin da aka kai wa bututun mai ya yi kamari, kamfanin zai dakatar da ayyukansa a jihar Bayelsa da ke yankin kudu maso gabashin kasar, domin neman hanyoyin daidaita wannan matsala.
Bututun man fetur da kamfanin Shell ya yi shirin rufewa, yana yankin kudu maso gabashin kasar, kuma tsawon bututun ya kai kilomita 97, wanda ya samar da man fetur da yawansu ya kai ganguna dubu 150 a kowace rana.
Haka kuma, kamfanin ENI ya ce, sabo da hare-haren 'yan fashin mai da ake kaiwa bututun mansa sun yi tsanani, shi ya sa yawan hasarar danyen mai da aka sata ya kai kashi 60 cikin 100 da aka samar a kowace rana. (Bako)