A cewar Gidan rediyon kasar jiya Talata, fiye da wakilai 50 ne daga kasashen duniya suke cikin kasar gabannin wannan taron da ake sa ran wakilai 100 ne daga kasashen duniya zasu halarta.
Matasan dake halartar taron sun ce, biyu daga cikin dalilan wannan taron shi ne a tattauna rawar da matasa za su taka wajen yakan mulkin danniya da kuma kare martaban kasar su.
Shugaban gamayyar kungiyar demokradiyyar matasa ta duniya Dimitris Palmkyris wanda dan asalin kasar Cyprus ne, ya ce matasan zasu samu sararin tattauna matsalolin dake damun su, wanda ya hada da siyasa da kuma tattalin arziki.
Ya ce, 'muna shirin karuwa da juna sosai daga wannan taron, ya kamata matasa su iya tsara makomar kasar su, don haka taron zai taimaka wajen shirya matasa su zama manyan gobe.'
Wakilai daga kasashen duniyan zasu ziyarci cibiyar taba sigari da kuma gonaki da matasa suka samu sakamakon gyara tsarin mallakan gonaki da kasar Zimbabwe ta yi.
Ganin wannan taro na gamayyar kungiyar demokradiyyan matasa ya zo kwanaki kadan da ranar nahiyar Afrika da ya kama ranar Jumma'a, matasa daga kasashen duniya sun yi kira ga shuwagabannin Afrika dasu hada kansu su wajen yaki mulkin mallakar dake kunno kai wanda yake son rusa cigaban da aka samu sakamakon yancin kai. (Fatimah)