Bankin na BAD ya sanar da cewa, a cikin tsarin tattalin arziki na nahiyar Afirka na shekara ta 2012, nahiyar ta kirkiro da guraban aiki guda milyan 16 kawai ga matasa masu shekaru 15 zuwa 24, wannan kuma tsakanin shekara ta 2000 zuwa ta 2008, duk da cewa, nahiyar na da bunkasar tattalin arziki mafi nagarta daga cikin kasashen duniya da kuma matasa da suka samu horo da ilmin zamani mai kyau.
Kirkiro da aikin yi mai amfani ga al'ummar matasa na Afirka wani babban kalubale ne, amma kuma wata hanya ce mai kyau sabili da zuwa gaba, kamar yadda marubutan rahoton suka sanar.
Wannan rahoto da aka ruwaito tare da hadin gwiwar bankin BAD, cibiyar kula da ci gaba da bunkasa ta OCDE, da kwamitin kula da tattalin arziki na MDD a nahiyar Afirka wato UNECA, da hukumar kula da da cigaba da bunkasar rayuwar al'umma ta MDD wato UNDP. Rahoton ya sanar da cewa, matasa wata dama ce da ci gaba nahiyar Afrika wajen bunkasa tattalin arziki nan gaba.
Rahoton ya sanar da cewa, wasu alkaluman na nuna cewa, za a fuskanci karuwar zaman kashe wando na matasa, idan har nahiyar Afirka ba ta gaggauta daukar hanyoyin samar da aikin yi ga matasa ba, ta yadda Afrika za ta amfani da yawan matasanta domin bunkasa tattalin arzikin nahiyar. (Abdou Halilou).