Wannan "sansanin kasa" na matasa da a shekarun baya ake kiransa "Sahel vert" a wannan karo an masa taken "Changer notre monde", wato " mu canza duniyarmu"
A tsawon wannan haduwa ta mako daya, matasan kasashen biyu za su dasa itatuwa 7000 a wasu wuraren da aka kebe.
Ministan matasa da al'adun kasar Nijar, Hassan Kounou ya shugabanci bikin kaddamar da wannan haduwa, haka kuma ministan ya nuna cewa wannan haduwa za ta taimakawa matasan sada zumunci da yin musanyar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi yaki da fari, wasannin motsa jiki, tsabtace muhalli, warware rikici ta hanyar sulhu da kuma batun yaki da ciwon sida. (Mamane Ada)