Dalilin shirya wannan dandali a karo na biyu a wannan watan na Yuni shi ne domin ana son shirya taron ministoci karo na biyar na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a watan Yuli mai zuwa, don haka wannan dandalin yana da muhimmanci sosai, musamman ma a fannin cudanya tsakanin matasa na bangarorin biyu a karkashin jagorancin manyan tsare-tsaren dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.
Babban taken dandalin da ya hada wakilai daga kasar Sin da kasashen Afrika 38 da yawansu ya kai 200 shi ne "hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da cigaban matasa".
A lokacin bikin bude dandalin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya nuna muhimmancin dandalin sosai, da ya ce, "Shirya dandalin shugabannin matasa na kasar Sin da kasashen Afirka yana da babbar ma'ana a tarihin cudanya tsakanin matasan kasar Sin da kasashen Afirka, shi ma yana da ma'anar musamman a tarihin dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wato ya dace da bukatun cigaban hadin gwiwa tsakaninsu. Haka kuma ya nuna cewa, matasa suna yin kokari matuka domin kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka tare da tabbatar da wadatuwa a kasashensu."
Zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yana da dogon tarihi, bangarorin biyu suna goyon baya da taimakawa juna, abin da yasa suke samun cigaba tare yadda ya kamata. A yayin bikin bude dandalin, shugabannin jam'iyyun siyasa da gwamnatoci na kasashen Afirka kamar su Tanzaniya, Namibiya, Zambiya da Afirka ta kudu sun nuna cewa, cigaban kasar Sin bai kawo barazana ga sauran kasashe ba, a madadin haka ma, ya samar da dama ga sauran kasashen duniya, musamman ma ga kasashen Afirka, haka kuma, muhimmancin da matasa ke da shi yana kara karuwa a kwana a tashi.
Dangane da wannan batu, babbar sakatariyar jam'iyyar Swapo ta kasar Namibiya Pendukeni Livula-Ithana ta fadi cewa, "Matasa na wakiltar makomar kasashenmu ne, haka kuma suna wakiltar makomar duniya baki daya. Shi ya sa, ina fatan wakilai mahalartan dandalin za su iya daukar hakki bisa wuyansu, ta yadda za su taimaka wa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. A yayin wannan dandalin, za mu kara mai da hankali kan batutuwan da suka shafi fahimtar juna wajen siyasa, cigaban tattalin arziki, cudanyar al'adu da tabbatar da dauwamammen cigaba. Ina sa rai cewa, za a samu babban sakamako a yayin dandalin."
Bisa bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, matasa suna kara ba da gudumuwa wajen gina kasashe da cigaban zamantakewar al'umma. Jia Qinglin ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin za su cigaba da nuna goyon baya ga cudanya da hadin gwiwa tsakanin matasan kasar Sin da kasashen Afirka saboda hakan zai taimaka wajen ingiza zaman lafiya, zaman karko da cigaban tattalin arziki a duk fadin kasashen duniya. Ya ce, "Ya kamata matasan kasar Sin da kasashen Afirka su kara himma domin kara karfafa zumuncinsu, ina fatan matasan kasar Sin da kasashen Afirka za su nuna kwazo da himma kan fannoni uku, wato kara bunkasa zumuncin gargajiya, ingiza hadin gwiwa tsakaninsu tare da yin kokarin kiyaye zaman lafiya da adalci tsakanin kasa da kasa."(Jamila)