Mr Kamwi ya ce, a kwanakin baya, dalibai 970 daga makarantu 2 dake birnin Windhoek da arewancin kasar sun kamu cutar mura, an yi bincike kan 31 daga cikinsu. Bisa sakamakon da aka samu, an tabbatar da cewa, 29 daga cikin wadannan mutane 31 sun kamu da cutar murar H1N1. Sabo da haka, ana sa ran cewa, yawancin daliban sun kamu da cutar murar H1N1.
Ban da wannan, a wannan mako, an rufe wata makarantar makahi dake birnin Windhoek na kasar, domin an gano wasu fiye da 60 da suka kamu da cutar mura a makarantar. Mr Kamwi ya bayyana cewa, yanzu dai an riga an killace yaduwar cutar kuma an kai wadanda suka kamu da cutar zuwa asibiti.(Zainab)