Mulet ya bayyana hakan ne yayin wani taron 'yan jaridu da aka shirya, yana mai cewa, bayan kwamitin sulhu ya kada kuri'a kan lamarin, MDD za ta tura sojojin zuwa Mali a watan na Yuli, wadanda kuma ake sa ran za su taimakawa mahukuntan kasar, wajen daukar matakan soja, da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasar. Ana dai sa ran za a jibge mafiya yawan dakarun ne a arewacin kasar ta Mali.
Bugu da kari, Mulet ya ce, kwamitin sulhu da kasashe membobin MDD, dama sauran kasashen duniya baki daya, na matukar goyon bayan kasar ta Mali, a kokarin ta na dawo da cikakken 'yankin kasar hannun halastacciyar gwamnati.
Don gane da wannan batu, shi ma ministan tsaron kasar Faransa ya bayyana a ranar 12 ga wata cewa, Faransa za ta kawo karshen matakan soja da take dauka a Mali, nan da makwanni uku. Wannan dai mataki na zuwa ne, daidai gabar da ake ci gaba da kokarin yaki da dakarun 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayi dake arewacin kasar ta Mali.(Fatima)