Xiao Hongyu,'yar wasan kasar Sin wadda ke kare kambi a wasan ajin masu nauyin kilogaram 48 na ajin mata, ta sake zama zakara bayan nasarar da ta yi a shekaru 2 da suka wuce, a gasar Universiade da ta gudana a birnin Shenzhen na kasar Sin.
'Yar wasan ta karya matsayin bajinta na gasar Universiade bisa baki dayan nauyin da ta dauka na kilogiram 187, sai dai a cewarta ba ta ji dadin ganin yadda ta kasa karya matsayin bajinta a fannin wasan daga nauyi na cirawa da dagawa ba.
Wannan 'yar wasa mai shekaru 22 a duniya ta ce bayan wannan wasa za ta shirya, domin fuskantar wasannin kasar Sin da za a gudanar a lardin Liaoning na kasar Sin a watan Satumba mai zuwa. Ta kara da cewa, bayan wannan wasa akwai yiwuwar ta yi ritaya daga fagen wasanni.
Har ila yau, a wasan daga nauyi na 'yan kilogiram 56 ajin maza, dan wasan kasar Sin Xu Jingui, shima ya samu lambar zinariya bisa nauyin da ya daga har kilogiram 264 nan take.