Wani zaman taro na kungiyar tattalin arzikin kasashen dake tsakiyar Afrika (CEEAC), da ya gudana a ranar Lahadi a birnin Addis-Ababa na kasar Habasha kan rikicin kasar Afrika ta Tsakiya CAR, ya dauki matakin yin matsin lamba ga tsohon shugaban kungiyar 'yan tawayen Seleka kuma shugaban rikon kwarya Michel Djotodia domin jituwa tare da faraministansa Nicolas Tiangaye, a wani labari na kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu. Duk da cewa, ya cigaba da rike mukaminsa, bayan kama ikon Djotodia a ranar 24 ga watan Maris a Bangui, Nicolas Tiangaye wanda aka nada bisa dalilin yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Libreville na kasar Gabon ta ranar 14 ga watan Febrairu, na fama da barazana kan mukaminsa tun lokacin amincewar baya bayan nan na kwamitin wucin gadi na kasar (CNT) da Alexandre Nguendet ke jagoranta, wani na hannun damar tsohon shugaban 'yan tawaye bisa wani yunkurin da ake na kifar da gwamnatinsa.
A cikin aikinsa na shiga tsakani, gungun shugabannin kungiyar CEEAC a karkashin jagorancin shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno, ya bukaci a girmama yarjejeniyar da aka cimma ta Libreville da ta baiwa madafun iko ga gwamnatin wucin gadi bisa wa'adin watanni 18.
Haka kuma taron ya jadadda muhimmancin gaggauta tura karin sojoji na tawagar dakarun kasa da kasa na tsakiyar Afrika (FOMAC) zuwa dubu biyu da za su hada na tawagar kungiyar CEEAC domin karfafa zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya (MICOPAX) da aka kiyasta zuwa sojoji dubu daya da dari shida. (Maman Ada)