Shugaban wucin gadin kasar Afrika ta Tsakiya CAR, Michel Djotodia ya isa birnin Libreville na kasar Gabon a ranar Laraba da yamma, duk da cewa, ba'a bayyana tsawon lokacin da wannan ziyara za ta kwashe ba. Shugaban kasar ta Afrika ta Tsakiya ya samu tarbo daga faraministan kasar Gabon, mista Raymond Ndong Sima a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Leon Mba dake birnin Libreville.
A yayin wannan ziyara ta farko a kasar Gabon a matsayinsa na shugaban mulkin wucin gadi a CAR yau da watanni uku, tsohon jagoran 'yan tawayen Seleka, Michel Djotodia ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba.
Wannan ziyara kuma ta zo kwanaki kadan kafin wani zaman taron shugabannin rundunar sojojin kasashe mambobin kungiyar tattalin arzikin kasashen dake tsakiyar Afrika (CEEAC) da za'a bude ranar Jumma'a a Libreville, domin mai da hankali kan matsalar tsaron kasar.
Tun bayan taron N'Djamena na ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata, shugabannin kasashen kungiyar CEEAC sun dauki alkawarin tura karin sojoji fiye da 1500 daga cikin tawagar sojojin karfafa zaman lafiya a kasar Afrika ta Tsakiya (MICOPAX) domin kiyaye zaman lafiyar wannan kasa ta CAR. (Maman Ada)