Jami'an MDD sun yi kiran ga al'ummomin kasa da kasa a Talata ran 25 ga wata, da su taimakawa sabuwar tawagar MDD da ke kasar Mali da muhimman kayayyaki, a kokarin da ake na ganin majalisar ta taimaka wa kasar a shirinta na sasantawa.
Wakilin babban sakataren MDD mai kula da kasar Mali Bert Koenders, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa kwamitin sulhu na MDD bayani ta hoton bidiyo daga Bamako, babban birnin kasar Mali.
Jami'in ya kuma yi kira ga kasashen mambobin majalisar, da su bayar da gudumawar muhimman abubuwan da ake bukata, sojoji da jami'an 'yan sanda da muhimman kayayyaki ga sabuwar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke Mali (MINUSMA)
A watan Afrilu ne kwamitin sulhun ya amince da tura dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD 12,600 wadanda za su maye gurbin dakarun da ke karkashin jagorancin kungiyar AU da ke Mali (AFISMA).
Ita dai sabuwar tawagar ta MINUSMA, an dora mata nauyin taimakawa shirin siyasar kasar da ke yammacin Afirka wadda ke farfadowa daga tashin hankalin da ya faru tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen Azbinawa, lamarin da ya kai ga kauran dubban daruruwan mutane tun a watan Janairun shekarar 2012.
Yanzu dai ana sa ran canjin aikin da aka yi daga hannun tawagar AFISMA zuwa MINUSMA zai fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, lokacin da galibin sassan sojojin da ke cikin tsohuwar tawagar za su koma bangaren sabuwar tawagar, abin da ake ganin cewa, tawagar ta MINUSMA za ta zama tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta uku mafi girma. (Ibrahim)