in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da 'yan gudun hijirar Mali 174129 a Burkina-Faso, Nijar da Mauritania
2013-06-21 10:59:38 cri

Tun da 'yan shekaru da dama, kasar Mali kamar sauran kasashe na duniya ta yi bikin ranar 20 ga watan Yuni, ranar 'yan gudun hijira ta duniya. Bikin wannan shekarar 2013, na da muhimmancin ganin yadda maganar 'yan gudun hijira take tsakiyar batutuwa.

Wannan matsala na da nasaba da rikicin tsaro da na jama'a da wannan kasa take fama da shi tun cikin lokacin watan Janairun shekarar 2012. Lokaci mai muhimmanci ga duk mutanen kasar Mali domin a cikin wannan lokaci ne kungiyoyin ta'addanci da 'yan tawaye suka dauki niyyar yin kaka gida bisa kashi uku cikin kashi hudu na fadin wannan kasa. Wannan al'amari ya janyo ficewar al'ummomin wadannan yankuna da aka mamaye. Dalilin haka ne, 'yan kasar Mali da dama suka kaura zuwa kasashen dake makwabtaka da kasarsu. Bisa kididdigar da cibiyar MDD kan harkokin jin kai (OCHA) ta bayar, an ce, kimanin 'yan gudun hijira na kasar Mali 174129, aka tabbatar suke zaune a kasashen Burkina-Faso, Nijar da Mauritania tun lokacin barkewar wannan rikici na arewacin kasar Mali a cikin watan Janairun shekarar 2012. A gaban wannan matsala ta kasar Mali, babbar kungiyar 'yan gudun hijira ta duniya (HCR) ta lura da tsara wasu matakan gaggawa bisa shirin yiyuwar tura sojoji domin murkushe wadannan kungiyoyi masu makamai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China