Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kafa wani kwamiti na musamman da zai nazarci bukatar hana yaduwar bindigogi a kasarsa, biyowa bayan kashe-kashen rayuka da ke aukuwa, sakamakon yawaitar bindigogin a hannun fararen hular kasar. Kwamitin wanda mataimakin shugaban kasar Joe Biden zai jagoranta, zai ba da shawarwari ga gwamnati, kan hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da kudirorin dakile yaduwar bindigogin, bayan harbin kan-mai-uwa-da-wabi, da wani matashi yayi kan wasu 'yan makaranta a baya-bayan nan a garin Newtown dake jihar Connecticut. Yayin da yake bayyana kafa kwamitin a fadar White House ranar 19 ga watan nan, shugaba Obama ya ce, ko da yake mahawara kan batun mallakar bindiga za ta dade tana janyo musayar ra'ayi, duk da haka, wajibi ne a dauki matakan da suka dace, domin kaucewa asarar rayuka da 'yan bindiga dadi ke haifarwa a kasar.
"Kasancewar wannan batu mai sarkakiya ba zai zamo dalili na kyale wannan matsala tana ci gaba ba, don haka zan yi amfani da dukkanin ikona, wajen hana sake faruwar irin wannan annoba a nan gaba." In ji shugaba Obama.
Ko da yake dai shugaban na Amurka ya yarda cewa, babu wata hanya daya tilo da za ta kai ga warware matsalar barna da mallakar bindigogin ke haifarwa, a hannu guda, ya jaddada bukatar daukar manyan matakan da suka wajaba, ciki hadda batun ilmantar da al'umma, da ba da kulawa ga harkokin lafiyar kwakwalwa, da a wasu lokuta ke haifar da wannan matsala. Daga nan sai shugaba Obama ya bayyana kyakkyawan fatansa ga kwamitin, wanda ya ce, zai fidda kudirorin doka da shawarwarin da suka shafi wannan batu a watan Janairu mai zuwa, yayin da shi kuma a nasa bangare, zai yi iyakacin kokarinsa, wajen nemawa kudirin dokar hana yaduwar bindigogin goyon baya a majalisar dokokin kasar.(Saminu)