in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya yaba wa gudummawar kamfanonin Sin wajen kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin Nijeriya
2013-03-16 17:18:20 cri
Ranar 14 ga wata, shugaba Goodluck Jonathan na kasar Nijeriya ya yi taron bita tare da kamfanonin kasashen waje, ciki har da kamfanin CCECC, inda ya yaba wa kokari da gudummawar da kamfanin CCECC da sauran kamfanonin kasar Sin suke bayarwa ba tare da kasala ba wajen sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar ta Nijeriya.

A wannan rana, Goodluck Jonathan, da wasu ministocin gwamnatin da kuma wakilan ma'aikatan bankuna da na masana'antun kasashen waje sun yi taron bita, inda suka tattauna yadda za a gudanar da muhimman ayyukan more rayuwar al'umma da raya birnin Abuja, hedkwatar kasar yadda ya kamata. Goodluck Jonathan ya ce, nasarorin da kasarsa ta samu a shekarun baya ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar sun dogaro da goyon baya daga shahararrun kamfanonin kasashen waje. Ya nuna godiya ga kamfanin CCECC bisa gudummawarsa wajen gudanar da muhimman ayyukan more rayuwar al'umma da bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar.

Mista Cao Baogang, shugaban kungiyar harkokin kasuwanci ta kasar Sin a Nijeriya kuma babban darektan kamfanin CCECC ya ce, a cikin shekaru sama da 30 bayan da kamfaninsa ya shiga Nijeriya, yana bin manufar neman samun moriyar juna da bunkasuwa tare. Ya kara da cewa, kamfaninsa zai ci gaba da raya kansa ta hanyar da ta dace da halin da ake ciki a wurin, a kokarin samar da guraben aikin yi a wurin, tare da kara azama kan bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Nijeriya.

Yanzu kamfanin CCECC yana shimfida hanyoyin dogo na zamani da fadada gine-ginen tashi da saukar fasinja a Nijeriya.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China