An bai wa Goodluck Jonathan iznin shiga babban zaben shugaban kasa a shekarar 2015
Ranar 1 ga wata, wata babban kotun tarayyar kasar Nijeriya da ke birnin Abuja, hedkwatar kasar ta yanke hukunci kan karar da aka kai game da hana shugaba Goodluck Jonathan na kasar ya shiga babban zaben shugaban kasar a shekarar 2015.
Kotun ta yanke hukuncin cewa, ko da yake Goodluck Jonathan ya zama shugaban kasar a watan Mayu na shekarar 2010 bayan da marigayi Umaru Musa Yar'Adua, shugaban Nijeriya na wancan lokaci ya rasu sakamakon ciwo ba zato ba tsammani, kuma bisa dalilin ya sa wannan majalisar dokokin kasar ta bukace shi ya zama shugaban kasar, don haka bai hau kan kujerar shugaban kasar ta hanyar shiga zabe ba, kuma bai fara wa’adin aikinsa a matsayin shugaban kasar ta Nijeriya a hukumance daga wancan lokaci ba. Kotun na ganin cewa, wa’adin aikin shugaba Goodluck Jonathan na farko ya fara ne daga watan Mayu na shekarar 2011, zai kare a shekarar 2015, don haka aka ba shi iznin shiga babban zaben shugaban kasar a shekarar 2015.
A watan Maris na shekarar 2012, Cyriacus Njoku, dan jam’iyyar PDP, wadda ke mulkin kasar, ya gabatar da karar cewa, kundin tsarin mulkin kasar Nijeriya ta haramta wa shugaban kasar da ya yi mulkin kasa fiye da wa’adi guda 2. Njoku ya kuma bukaci a soke wa Goodluck Jonathan iznin shiga babban zaben shugaban kasar a shekarar 2015.(Tasallah)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku