Yace yanzu dangantaka tsakaninsu na cikin yanayi mafi kyau a tarihi. Dangane da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a kasarsa, ministan ya ce Tanzaniya na nuna kyakkyawan fata kan zuwansa.
A gun taron 'yan jaridu da aka shirya a birnin Dar es Salaam, hedkwatar kasar, Bernad Membe ya bayyana cewa, Tanzaniya tana alfahari sosai kasancewa kasa ta farko da shugaba Xi zai kai ziyara a nahiyar Afirka. A cewarsa, sabon shugaban kasar Sin zai kai ziyarar aikinsa karo na farko a kasashen Afirka, inda hakan ke nufin cewa, Sin tana dora muhimmanci sosai kan bunkasa dangantakar abota dake tsakaninta da kasashen Afirka.
Bernad Membe ya jaddada cewa, tarihi ya nuna cewa, ko kasashen Afirka suna cikin yanayi mai kyau ko mai tsanani, kasar Sin ta nuna ita aminiyarsu ce a ko da yaushe.
Ministan ya kara da cewa, a wannan sabon zamani, dangantaka tsakanin Sin da Tanzaniya tana bunkasa lami lafiya, musamman ma a fuskar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu dake bunkasa cikin sauri.(Fatima)