Jakada Tian yana ganin cewa, samun moriyar juna ta hanyar hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, wata babbar alama ce ta bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu. Bisa alkaluman da hukumar kwastan ta Sin ta bayar, an ce, a shekarar 2012, jimillar kudin cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai kimanin dala biliyan 60.
A cikin shekarun da suka wuce, Sin ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ga kasar Afirka ta Kudu, haka ma ita ma kasar ta Sin a nahiyar Afirka.
A sa'i daya, Tian ya jaddada cewa, karfafa mu'amala a fannin al'adu, ya dasa wani tushe mai kyau ga bunkasar dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Dadin dadawa, Tian ya kara da cewa, bunkasuwar kasashen Sin da Afirka ta Kudu na kama da juna, haka ma burinsu da tsare-tsare na samun bunkasuwa. A sabili da haka, suna da moriyar iri daya a fannonin tabbatar da zaman lafiya, da sa kaimi ga hadin gwiwa, da kuma neman samun ci gaba. Kasashen biyu suna kyautata dangantaka tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)