in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bar kasar Rasha zuwa Tanzaniya a ziyarar aiki da yake yi
2013-03-24 16:32:16 cri
A ranar Lahadi 24 ga wata, bayan kammala ziyararsa a Rasha, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Moscow zuwa kasar Tanzaniya.

Rasha ta kasance kasar ta farko da shugaba Xi ya kai ziyara bayan kama aiki.

A ranar Jumma'a 22 ga wata, shugaba Xi ya isa birnin Moscow, inda ya yi shawarwari da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, tare da yin musayar ra'ayoyi kan dangantaka tsakanin Sin da Rasha, da wasu muhimman batutuwan duniya da na shiyya-shiyya. Shugabannin biyu sun cimma matsaya daya kan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni.

Dadin dadawa, shugabannin biyu sun rattaba hannu kan wata hadaddiyar sanarwa dangane da hadin gwiwa da samun moriyar juna, da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, inda aka tabbatar da hanyar da za a bi wajen yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha. Wannan ya bayyana matsayin da kasashen biyu ke kasancewa don gane da hadin gwiwa tsakaninsu da kuma ragowar muhimman harkokin duniya.

A ranar Asabar 23 ga wata, shugaba Xi ya ba da jawabinsa a kwalejin nazari kan dangantakar kasashen duniya dake Moscow, inda ya bayyana ra'ayinsa kan yanayin da duniya ke ciki da manufar da kasar Sin take gudanar a fannin diplomasiyya da kuma kokarin bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Rasha.

Kafofin yada labaru na ganin cewa, wannan ziyara ya zuba sabon kuzari ga bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha cikin yanayi na lumana.

Bayan ziyararsa a Tanzaniya kuma, shugaba Xi zai kai ziyara a kasar Afirka ta Kudu, da Jamhuriyyar dimokuradiyyar Kango, tare da halartar taron shugabannin kasashen BRICS karo na biyar da za a yi a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China