Shugaba Kikwete ya bayyana cewa, Tanzaniya da Sin suna cimma matsaya kan harkokin duniya da dama, kuma suna nuna wa juna goyon baya a fannin diplomasiyya, tare da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata.
Dadin dadawa, shugaba Kikwete ya kara da cewa, jama'ar kasar suna nuna da kyakkyawan fata ga ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping. Shugaba Xi zai kai ziyara ta farko ne a kasashen Afirka, ciki da kasar ta Tanzaniya, wannan ya yi nuni da cewa, sabuwar gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan bunkasa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen dake nahiyar Afirka da Sin.
Bugu da kari, shugaba Kikwete ya furta cewa, yana sanya ran yin shawarwari da shugaba Xi kan dangantaka tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin, da dai sauransu. Ya yi imani da cewa, ziyarar shugaba Xi za ta karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu da sauransu, ta yadda jama'arsu za su ci gajiyar hakan yadda ya kamata.(Fatima)