in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran ziyarar shugaba Obama za ta kara bunkasa hadin gwiwa tsakanin Amurka da Afirka ta Kudu
2013-06-26 10:03:22 cri

Ministan dangantakar kasa da kasa da hadin gwiwa na kasar Afirka ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane ya bayyana jiya Talata cewa, ziyarar da shugaban kasar Amurka Barack Obama zai kawo kasar Afirka ta Kudu za ta kara bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A yayin ziyarar, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, zai yi shawarwari da shugaba Obama a birnin Pretoria kan batutuwa da suka shafi dangantakarsu, cinikayya, kiwon lafiya, ilmi, tallafin samun bunkasa, zaman lafiya da tsaro, in ji Nkoana-Mashabane yayin wata ganawa da manema labaru a birnin Pretoria.

Matakan kasar Amurka dangane da kasashe dake kudu da yankin Sahara, wadanda shugaba Obama ya sanar a cikin watan Yunin shekarar 2012, na mai nunin cewa, Afirka na da muhimmanci matuka ga tsaro da wadatar al'ummar duniya baki daya, musamman ma ga kasar Amurkan kanta.

Amurka, babbar abokiyar cinikayya ce ga kasar Afirka ta Kudu, kuma ta ci gaba da kasancewa kan gaba a jerin abokan huldar cinikayya da zuba jari. Hakazalika, Amurka muhimmiyar kasuwa ce ga kayayyakin Afirka ta Kudu, kuma kasa ce da ake samun zuba jari daga waje kai tsaye. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China