Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya yi maraba da cimma matsaya guda tsakanin gwamnatin kasar Mali da kungiyoyin 'yan tawayen Azbinawa dake kasar, lamarin da ya kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da za su ba da damar dakatar da bude wuta, da gudanar da babban zaben kasar, tare da bude kofar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu bayan kammalar zaben dake tafe.
Wata sanarwa daga ofishin kakakin magatakardar MDD ta tabbatar da cewa, kungiyoyin 'yan tawaye na MNLA da HCA, sun amince da sanya hannu kan yarjejeniyar da suka cimma da tsagin gwamnati da maraicen ranar Talata a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso. Sanarwar ta kuma rawaito Ban Ki-Moon na kira ga bangarorin biyu, da su gaggauta aiwatar da shawarwarin da aka cimma, domin tabbatar da warware dukkanin takaddamar dake tsakaninsu cikin lumana.
A wani ci gaban kuma Mr. Ban ya jinjinawa kungiyar ECOWAS, sakamakon shiga tsakani da ta yi tare da kungiyar AU da MDD, matakin da ya taimaka har aka kai ga cimma wannan gagarumar nasara, yana mai cewa, MDD karkashin hukumominta da ragowar masu ruwa da tsaki, za su sanya kaimi wajen ganin an kai ga aiwatar da dukkanin shawarwarin da aka cimma. (Saminu)