in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kulla wata yarjejeniyar kafa kwalejin Confucius da kasar Nijeriya
2011-03-23 10:06:30 cri

Ranar Talata 22 ga wata da yamma a Abuja babban birnin kasar Nijeriya, Sin ta kulla wata yarjejeniyar kafa kwalejin Confucius da jami'ar ABU ta kasar.

Jakadan kasar Sin dake Nijeriya Deng Boqing, yayin da ya gana da mataimakin shugaban jami'ar ABU Abdullahi Mustapha ya nuna cewa, yanzu daliban kasar Sin hudu suna karatu domin kara ilmin harshen Hausa a jami'ar, ya yi imani da cewa, kafa ajin koyar da Sinanci wannan zai yi amfani ga kara fashimtar juna har da habaka zumunci tsakanin matasan kasashen biyu. Mustapha ya nuna matukar maraba ga hadin kai da bangarorin biyu za su yi, ya ce, Sin na da abubuwan koyi masu kyau ga Nijeriya, jami'arsa za ta koyon abubuwa masu inganci cikin hadin kai da bangarorin biyu za su yi. Ban da wannan kuma, yana fatan Sin za ta kafa kwalejin Confucius a kasar cikin hanzari, ta yadda daliban kasar za su koyon ilmin Sinanci mai inganci.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China