in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gabatar da alamar Confucius a Madagascar
2011-03-02 09:56:58 cri

Ranar Talata 1 ga wata a kasar Madagascar, jami'ar Antananarivo ta gabatar da alamar Confucius wani shahararren malami a tarihin kasar Sin da jami'ar horar da malamai ta lardin Jiangxi ta kasar Sin ta bayar. Dalibai da malamai kimanin 200 sun halarci bikin gabatarwa.

Wannan alama dake dab da kofar kwalejin Confucius na jami'ar Antananarivo tsayinta ya kai mita 2.6 wanda malaman jami'ar horar da malamai ta lardin Jiangxi suka tsara. Jakadan kasar Sin dake Madagascar Shen Yongxiang da shugaban jami'ar Antananarivo sun yi jagora wajen gabatar da alamar.

An labarta cewa, an kafa kwalejin Confucius din a watan Nuwamba na shekarar 2008 wanda ya kunshi ajin koyar da Sinanci guda tara. Kuma yana gabatar da kos din Sinanci na matakin farko, lafazin Sinanci, karanta Sinanci, saurari Sinanci, hira da Sinanci, nahauwun Sinanci, rubutun Sinanci, al'adun kasar Sin da dai sauransu. Yawan mutanen da suke koyon Sinanci a kwalejin ya haura 3000.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China