Masu aikin sa kai wadanda suke koyar da harshen Sinanci a jami'ar sun yi nune-nunen al'adun kasar Sin, kuma sun yi rawa mai taken "Hanyar dake sararin sama" ta kabilar Tibet. Ba ma kawai 'yan kallo sun ga tufafi iri iri na al'ummar kasar Sin ba, har ma sun kara sanin asalin al'adun kasar Sin ta hanyar kallon shirye-shirye iri iri dake nuna al'adun kasar Sin. Sannan rawar "Hanyar dake sararin sama" da aka yi bisa shugabancin shehun malama Jiang Lirong, wato shugabar kwalejin Confucius ta jami'ar Lagos ta samu karbuwa sosai daga wajen 'yan kallo.
Madam Jiang Lirong ta bayyana cewa, rawar da masu aikin sa kai suka yi ta samu karbuwa sosai daga wajen 'yan kallo fiye da dubu 2 na kasar Sin da na kasar Najeriya. Ta ci gaba da cewa, shirye-shirye na nune-nunen al'adun kasar Sin da kwalejin Confucius ta jami'ar Lagos ya yi sun kawo sabbin abubuwa ga 'yan kallo na wurin, kuma suna nuna sha'awarsu ga al'adun kasar Sin.
An shirya wannan biki ne cikin tsawon makonni biyu kawai bayan isar sabbin masu aikin sa kai na koyar da harshen Sinanci a kasar Najeriya. (Sanusi Chen)