in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta soki harin da aka kai a haraban ofishin MDD dake Somaliya
2013-06-21 10:53:35 cri

A jiya Alhamis 20 ga wata, kasar Afrika ta Kudu ta ce, abin kunya ne harin da wassu suka kai haraban gidajen ma'aikatar ofishin MDD dake Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya.

A cikin sanarwar da sashin kula da harkokin kasashen waje da hadin gwiwa ta kasar DIRCO ya fitar, ta nuna matukar damuwa game da wannan harin da aka kai a ranar 19 ga wata, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 15, ciki har da 'yan asalin kasar Afrika ta Kudu guda biyu wadanda har yanzu ba'a gane su ba, amma, ana kyautata zaton suna aiki ne karkashin ofishin wanzar da zaman lafiya a Somaliya na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, wato AMISOM.

Kasar Afrikan ta Kudu ta mika sakon ta'aziyarta ga MDD, gwamnatin kasar Somaliya, iyalan mamatan da sauran abokan arziki, musamman na kusa da wadanda suka rasa rayukansu, in ji kakakin wannan hukuma ta DIRCO Clayson Monyela.

Wannan harin ya zo ne a lokacin da ake lissafa cigaban da aka samu na zaman lafiya da karko ta bangaren walwala da tattalin arzikin al'umma a Somaliya, kuma ita kanta gwamnatin Somaliyan take cikin bukatar samun goyon bayan sauran kasashen duniya da hukumomi, ciki har da MDD, in ji kakaki Clayson Monyela, (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China