Mataimakin wakilin din din din na kasar Sin a MDD Wang Min shi ne ya bayyana hakan a gun taron kwamitin sulhu na MDD cewa samar da cikakken kwanciyar hankali da sake kafa kasar ta Afganistan zai dauki dogon lokaci ,wanda hakan ya bukaci gwamnatin kasar da jama'arta su dinga yin kokari, tare da kara samun tallafawa daga gamayyar kada da kasa.
Wang ya kara da cewa kasar Sin ta firgita da Allah wadai da kisan da aka yi wa tsohon shugaban kasar ta Afganistan kuma shugaban mai fafutukar kawo sulhu da 'yan Taliban Burhandi Rabbani .
Daga nan ya shaida cewar kasar Sin tana nuna cikakken goyon baya ga gwamnati da al'ummar kasar tare da fatan ganin an samu cigaba a kokarin da ake yi na tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kan al' umma.
Da yake tabo tsare tsare kan sake farfado da tattalin arzikin kasar ta Afganistan, Mista Wang ya ce, kasar Sin ta yi imanin cewa kamata ya yi duk bangarorin da abun ya shafa su mai da hankali kan ra'ayin gwamnati da al'ummar kasar tare da girmama 'yancin kai na kasar Afganistan.(Salamatu)