in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya karbi bakonci wakilin Sin kan hulda da kasashen Afrika
2013-06-20 10:48:05 cri

Shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir a jiya Laraba 19 ga wata, ya karbi bakoncin wakilin kasar Sin kan hulda da kasashen Afrika Zhong Jianhua, kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga ofishin jakadancin kasar Sin dake Khartoum, fadar gwamnatin kasar ta Sudan ta bayar wadda ta yi bayanin cewa, a lokacin ganawarsu, bangarorin biyu sun yi musanyar ra'ayi a kan dangantakar dake tsakanin kasar Sudan da Sudan ta Kudu.

Haka kuma duk a jiya Laraban, Zhong Jianhua ya tattauna da mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasar ta Sudan Nafie Ali Nafie, inda ministan harkokin wajen kasar Salah Wanasi da kuma jakadan kasar Sin dake Sudan Luo Xiaoguang dukkan su suka halarta.

A wani labarin kuma tun da farko sai da Mr. Zhong ya halarci taro karo na biyar na shawarwari da wakilan kasashen waje game da rikicin Darfur da aka yi a ranakun 16-17 ga watan nan a garin El Fasher, babban birnin jihar arewacin Darfur dake Sudan.

A lokacin wannan taro, cikin jawabinsa, Zhong ya ce, matsalar Darfur yana da sarkakkiya kuma ya shafi yanayin tsaro da kwanciyar hankali a yankin. Kasar Sin tana goyon bayan samar da zaman lafiya, tana kuma matukar son taimakawa, ta ga hakan ya tabbata tare da haifar da daidaito a wurin. A ranar 16 ga wata, Mr. Zhong ya gana da ministan harkokin kasashen waje na Sudan Ali Karti, ministan sha'anin man fetur Awad Ahmed Al-Jaz da kuma babban mai daidaitawa a rikicin Sudan ta Kudu Idris Abdul Ghader, inda a lokacin ganawar, aka yi musayar ra'ayi game da dangantakar dake tsakanin Sudan da kasar Sin da kuma dangantakar dake tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China