Yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, an yanke hukunci kan manyan jami'an jihohin kasar da kuma yaki da cin hanci ta hanyar internet.
Wadannan su ne sabbin ayyukan da aka gudanar a fannin yaki da cin hanci da rashawa a kasar, don haka jama'ar kasar suke sa rai ganin canji a wannan fanni.
Bisa la'akari da hali da ake ciki dangane da wannan batu, muhimmin zama na kwamitin ladabtarwa karo na biyu ya jawo hankalin kasar sosai.
Sharhin ya ce, ya kamata a kawar da dukkan wata hanyar yiwuwar wuce gona da iri, wajen yin amfani da iko don magance cin hanci da rashawa. Kamar yadda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a ranar 22 ga wata, ya ce, kamata ya yi a kara sa ido kan tafiyar da ikon mulkin kasar, da kuma yin amfani da iko yadda tsarin kasar ya tanadar.
Ya zuwa yanzu a duniya, babu wata kasa ko jiha da ta iya kawar da cin hanci ta hanya daya kawai wato yin bincike kan batutuwa da suka shafi karya dokoki.
Yayin da ake yaki da cin hanci, ya kamata a yi bincike kan batutuwa na aikata laifuffuka tare da kyautata tsarin kasar, musamman ma a fuskar kawar da yiwuwar wuce gona da iri wajen yin amfani da iko. (Zainab)