Jaridar People's Daily ta fitar da wani sharhi a ranar alhamis 17 ga wata cewa, ana mai da hankali sosai wajen tabbatar da zaman karko a kasar Mali, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ci gaba da ba ta taimako, ta yadda za a taimakawa kasashen Afrika wajen rage talauci da raya kasashe yadda ya kamata.
Sharhin ya nuna cewa, ana fuskantar kalubaloli da dama wajen warware rikicin kasar Mali dake da alaka da addini, kabila, zaman rayuwar jama'a, talauci da dai sauran bangarori. Ya kamata, a warware wannan rikici ta hanyar yin kokarin sa kaimi ga bunkasuwar kasashen duniya. Idan babu bunkasuwa to ba za'a samu zaman karko ba kuma halin da ake ciki zai kara tsananta. Rikicin dake barkewa a kasar Mali yana gargadi ga kasashen duniya cewa, kasa da kasa musamman MDD na da hakkin dake bisa kansu wajen samar da wani yanayi mai kyau wajen raya kasashen Afrika musamman ma kasar Mali.
Ban da haka, sharhin ya nuna cewa, ya kamata, kasashen duniya su kara taimakawa wajen inganta dunkulewar nahiyar tare kuma da tallafa musu wajen kara karfin samun bunkasuwa tare kuma da samar da yanayi mai kyau. (Amina)