Jaridar People's Daily ta bayar da jawabi a ran 17 ga wata cewa, ya kamata a dauki nauyin tabbatar da moriyar jama'ar kasar Sham da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya. Kasar Sin tana da matsayinta, kuma ta dauki matakai a kan wannan batu, ya kamata kasashen duniya su daidaita batun kasar Sham bisa wannan tushe.
Bayanin ya bayyana cewa, rikicin kasar Sham ya kawo mummunan tasiri sosai ga jama'ar Sham, kana ya zama kalubale mai tsanani a gaban gamayyar kasa da kasa. Ya kamata a yi Allah wadai da dukkan tashe tashen hankalin da ya rutsa da fararen hula a kasar, kuma dole ne a dakatar da duk wani tashin hankali cikin gaggawa. Don haka, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta tsaya kan matsayinta, kuma ta dauki matakai masu yakini.
Ban da haka kuma, bayanin ya ce, ya kamata a kawo karshen rikici cikin gaggawa, kuma ya fi kyau a yi hakuri da juna, daukar matakan soja domin hambarar da gwamnati ba hanya ce da ta dace ba. Idan aka yi kuskuren karya dokar MDD, to batun kasar Sham zai kara tsananta, kuma hulda a tsakanin kasa da kasa za ta lalace.(Lami)