A kwanakin baya, rukunin wakilan musamman na MDD da na kungiyar tarayyar kasashen Larabawa (AL) ya isa kasar Sham, domin ganawa da bangarori daban daban na kasar Sham kan shawarwarin da Kofi Annan ya gabatar na kawo karshen rikicin kasar Sham da kuma maganar tura 'yan kallo na kasashe daban daban zuwa kasar. Ko da yake ana ci gaba da samun rikicin tarzoma a birnin Dimashq. A ran 19 ga wata, sojojin gwamnatin kasar Sham da kungiyar adawa sun yi musayar wuta mai tsanani a birnin Dimashq, lamarin da ya kasance mafi tsanani da ya barke a tsakaninsu tun daga wannan shekara a birnin.
Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta yi sharhi a ran 21 ga wata cewa, an dora wa Kofi Annan nauyin shimfida zaman lafiya a kasar Sham ne bayan da kwamitin sulhu na MDD ya ki amince da daftarin da zai kawo karin barazana ga zaman rayuwar jama'ar kasar Sham, kuma shi ne sakamakon da kasashen Sin da Rasha da kuma sauransu suka yi ta kokarin neman bakin zaren daidaita batun Sham ta hanyar siyasa, shi ya sa, ya samu goyon baya sosai daga MDD da kungiyar AL da kuma gwamnatin kasar Sham. Amma, wasu kasashen duniya suna ci gaba da kokarin yin juyin mulki a kasar Sham, hakan zai sa rikicin kasar ya kara tsananta.
Jaridar Vatan Gazetesi ta kasar Oman ta bayar da bayani a kwanan baya, inda ta nuna yabo ga shawarwarin da kasashen Sin da Rasha suka bayar don kawo karshen rikicin kasar Sham.
Bayanin ya ce, kasashen Sin da Rasha sun bayar da shawarwarin kawo karshen rikicin kasar Sham domin kubutar da kasar daga wahalhalu da kare rayukan jama'a da kuma dukiyoyinsu. Idan wasu kasashen dake nuna goyon baya ga kungiyar adawa ta kasar Sham suna son daidaita batun kasar, ya kamata su mayar da martani mai yakini ga kokarin da kasashen Sin da Rasha ke yi, domin daina tada tashin hankali domin kawo karshen rikicin kasar Sham ta hanyar diplomasiyya.(Lami)