Wani dan jarida ya yi tambaya cewa, a halin yanzu tattalin arzikin Sin ya ragu amma tattalin arzikin Amurka ya fara samun farfadowa, ko wannan zai yi tasiri ga tattaunawar batun tattalin arziki da cinikayya da tsara matakai yayin da shugabannin kasar Sin da ta Amurka suke ganawa?
Game da wannan, Hong Lei ya bayyana cewa, yanzu an raya tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata. Hazakila kuma, a ganin kasar Sin, farfadowar tattalin arzikin Amurka za ta kawo moriya ga kasar Amurka, har ma ga tattalin arzikin duniya gaba daya.
Hong Lei ya kara da cewa, a kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga shugaban kasar Amurka Barack Obama, inda ya nuna cewa, kamata ya yi kasashen biyu su yi shawarwari cikin adalci don magance yadda ake juya batun tattalin arziki zuwa batun siyasa, da zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu. Ta haka, za a amfana wa jama'ar kasashen biyu, kana za a taimakawa samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Zainab)