Kakakin rundunar tsaron na hadin gwiwwa JTF Laftanr Kanar Sagir Musa a cikin wata sanarwa, ya ce wannan doka an saka shi ne domin ya ba da sarari ma jami'an tsaro su samu nasarar wannan samame da suka kaddamar a kan 'yan ta'addan.
Shi dai wannan dokar hana fitar an saka shi ne a unguwannin Gamboru, Mairi Kuwait, Bakin Kogi, Kasuwan Shanu, Ruwan Zafi, 202 Quarters, Dikwa Quarters, Low-Cost Sinimari, Gidajen Kwana na 505, Chad Basin, Gidajen Kwana na 303 da kuma unguwannin dake han hanyar Baga, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Don haka rundunar tsaron na JTF ta bukaci al'umma da su ci gaba da bata hadin kai ta hanyar bata muhimman bayanai kuma akan lokaci.
A ranar Talatan makon jiya ne dai Shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a jihohi 3 na Adamawa, Yobe da kuma ita kanta Borno ganin cewa a watan jiya ya yi kokarin ganin 'yan kungiyar sun dakatar da bude wuta domin a sulhunta a kuma masu ahuwa ammam hakan yaci tura. (Fatimah Jibril)