in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakurun tsaron Nigeriya sun cafke 'yan ta'adda 65 a Maiduguri
2013-05-19 16:19:41 cri
A ranar Asabar 18 ga wata rundunar tsaro na musamman na Nigeriya dake aiki a garin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar a yanzu haka sun samu nasarar damke wadansu 'yan ta'adda guda 65, a cikin wata sanarwar da kakakin rundunar tsaron kasar brigediya janar Chris Olukolade ya fitar ma manema labarai a Abuja wanda ya yi bayanin cewa wadanda aka kama suna kokarin kutsa kai ne a cikin garin Maiduguri sakamakon lalata sansanin su da aka yi a lokacon samame na musaman da jami'an tsaro suka yi.

Sanarwar ta yi bayanin cewa wannan samame yanzu aka fara a cikin ayyukan da rundunar ta dauka na raba garin da wadannan miyagu, kuma wadanda aka kama suna hannun hukuma a na masu tambayoyi.

Sanarwa ta yi bayanin cewa yawancin sansanin da rundunar tsaron ta gano ta kuma kai ma samame an fahimci cewa 'yan ta'addan sun ankara za'a zo wajen shi ya sa suka tsere daga wurin suna kokarin komawa cikin gari, don haka wadannan wurare rundunar tsaro ta maida shi a karkashin ikonta.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar tsaron kasar baki daya dake Abuja ta kara bada umurnin sojojin su kara bada himma wajen takura ma 'yan ta'addan sosai. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China